[ { "title": "Elisha ya amsa", "body": "Elisha ya na amsa tambayar sarkin Isra'ila." }, { "title": "Ko ka kashe bayin da ka kama da bãkanka da kuma takobinka? ", "body": "Elisha ya yi amfani da wannan tambayar don tsauta wa sarki ya kuma ce masa kada ya kashe waɗannan mutanen. Kalmomin \"takobi da baka\" kalmomi ne na yaƙe-yaƙe waɗanda sojoji suke amfani da takuba da baka da kibau. Ana iya\nrubuta wannan azaman sanarwa. AT: \"Ba za ku kashe mutanen da kuka kama a yaƙi ba, don haka kar ku kashe waɗannan mutanen.\" ( (Duba: figs_rquestion da figs_metonymy)" }, { "title": " da takobinka da bakanka", "body": "Waɗannan makaman da ake anfani da su ne a yaƙi. AT: \"a yaƙi da takobinka da bakanka\" (Duba: figs_explicit)" }, { "title": "ka ba su gurasa da ruwa domin su ci su sha", "body": "A nan \"gurasa\" na nufin abinci. AT: \"ka ba su abinci da ruwa domin su ci su sha,\" (Duba: figs_synecdoche)" }, { "title": "je wurin shugabansu.", "body": "Wannan na nufin sarkin Aram." }, { "title": "sarki ya shirya abinci sosai domin su,", "body": "Sarki yasa bayinsa su su shirya masu abinci. Bai shirya abincin da kansa ba. AT: \"Sai sarkin yasa bayinsa suka shirya masu abinci da yawa\" (Duba: figs_metonymy)" }, { "title": "Waɗannan ƙungiyoyin", "body": "\"Waɗannan ƙungiyoyin\"" }, { "title": "ba su daɗe ba sosai a Isra'ila.", "body": "Wannan na nufin ba su sake kai wa Isra'ila hari da wuri ba. AT: \"suka daina kai wa ƙasar Isra'iala hari na ɗan tsawon lokaci\" (Duba: figs_explicit)" } ]